Tsohon Dan Siyasa Kuma Dattijon Arewa, Alh Musa Musawa Ya Rasu
Zababben shugaban kasar Najeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rashin babban dattijo, Alhaji Musa Musawa. An haife shi marigayi Alh. Musawa a ranar 1 ga Afrilu, 1937 kuma ya kasance mai watsa labarai, jami'in diflomasiyya kuma hazikin dan siyasa. Marigayi Alh. Musa ya rasu ne a ranar Talata bayan ya sha fama da rashin lafiya kuma ya rasu ya bar ‘ya'ya da dama da sauran ‘yan uwa da suka hada da mataimakiyar kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Hajiya Hannatu Musawa. A cikin wata sanarwa da kakakin zababben shugaban, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, "Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin dan jihar Katsina a matsayin daya daga cikin mataimaka na karshe na masu fafutukar kwato ‘yancin Najeriya, hakika kuma ya kasance dan siyasa mai ci gaba kuma mai fa’ida. A lokacin Alh Musa ya raye da kuriciya, ya hada kai da ’yan uwa masu tunani iri daya a rusasshiyar kungiyar Arewa Elements Progressive Union (NEPU) d...