Tsohon Dan Siyasa Kuma Dattijon Arewa, Alh Musa Musawa Ya Rasu
Zababben shugaban kasar Najeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rashin babban dattijo, Alhaji Musa Musawa.
An haife shi marigayi Alh. Musawa a ranar 1 ga Afrilu, 1937 kuma ya kasance mai watsa labarai, jami'in diflomasiyya kuma hazikin dan siyasa.
Marigayi Alh. Musa ya rasu ne a ranar Talata bayan ya sha fama da rashin lafiya kuma ya rasu ya bar ‘ya'ya da dama da sauran ‘yan uwa da suka hada da mataimakiyar kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Hajiya Hannatu Musawa.
A cikin wata sanarwa da kakakin zababben shugaban, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, "Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin dan jihar Katsina a matsayin daya daga cikin mataimaka na karshe na masu fafutukar kwato ‘yancin Najeriya, hakika kuma ya kasance dan siyasa mai ci gaba kuma mai fa’ida.
A lokacin Alh Musa ya raye da kuriciya, ya hada kai da ’yan uwa masu tunani iri daya a rusasshiyar kungiyar Arewa Elements Progressive Union (NEPU) domin fafutukar kwato ‘yancin kai da ‘yantar da al’ummarmu baki daya.
“A shekarun baya bayan samun ‘yancin kai Alhaji Musa Musawa ya ci gaba da hada kai da kungiyoyi masu ci gaba a ciki da wajen siyasa domin ciyar da talakawa da wadanda ake zalunta gaba a cikin al’umma.
“Ya kasance dan siyasa mai ci gaba wanda ya biya hakkinsa a matsayinsa na mai kishin kasa. Najeriya ta yi hasarar hazikin da kuma za mu rasa shawararsa ta uba a daidai lokacin da muka fi bukata,” inji Tinubu.
Zababben shugaban kasar ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa dattijon ya kuma yafe masa kurakuransa. ya kuma bai wa iyalansa ta’aziyyar da ake bukata a lokacin da suke cikin bakin ciki.
Rahoto daga Muhammad Isah Ramat
Talata, 7 Maris 2023
Ramat Unlimited ®
Comments
Post a Comment