Posts

Showing posts from March, 2025

Wata Mata A Kaduna Ta Neme Kotu Ta Raba Auran Ta Sabida Yawan Son Jima'i Na Mijinta

Image
Wata mata mai shekaru 37, Linda Stephen, a ranar Talata, ta garzaya wata kotun gargajiya a Kaduna, inda ta nemi kotu ta raba auran dake tsakanin ta da mijinta, Felix Stephen domin yawan sha’awar jima’i.  A cikin karar da ta shigar, Mrs Stephen, wata mazauniyar Ungwan Sunday a Kaduna, ta  zargi mijin nata neh da dukan ta a duk lokacin da ta ki amincewa da ta kwanta da shi.    Ta shaida wa kotun cewa shekarun su shida wanda a yanzu ba ta da sha’awar auren domin ba za ta iya jurewa yawan bukatar mijin nata ba. A bayanin Mrs Stephen,  “Ina kira ga kotu da ta raba auren domin ba zan iya jure yawan sha’awar jima’i ba, Minina yana son jima’i da yawa, kuma ba zan iya jurewa ba, yawancin lokaci yakan yi jima'i da ni tun daga tsakar dare har zuwa safiya, ko da ina kuka, ba zai daina ba".  Stephen, a martanin da ya mayar, ya shaida wa kotun cewa yana son matarsa.   Ya kuma roki kotun da ta taimaka masa wajan kwantar wa da matan sa hankali, kada ta kashe aura...