Wata Mata A Kaduna Ta Neme Kotu Ta Raba Auran Ta Sabida Yawan Son Jima'i Na Mijinta

Wata mata mai shekaru 37, Linda Stephen, a ranar Talata, ta garzaya wata kotun gargajiya a Kaduna, inda ta nemi kotu ta raba auran dake tsakanin ta da mijinta, Felix Stephen domin yawan sha’awar jima’i.

 A cikin karar da ta shigar, Mrs Stephen, wata mazauniyar Ungwan Sunday a Kaduna, ta  zargi mijin nata neh da dukan ta a duk lokacin da ta ki amincewa da ta kwanta da shi.  

 Ta shaida wa kotun cewa shekarun su shida wanda a yanzu ba ta da sha’awar auren domin ba za ta iya jurewa yawan bukatar mijin nata ba.

A bayanin Mrs Stephen,  “Ina kira ga kotu da ta raba auren domin ba zan iya jure yawan sha’awar jima’i ba, Minina yana son jima’i da yawa, kuma ba zan iya jurewa ba, yawancin lokaci yakan yi jima'i da ni tun daga tsakar dare har zuwa safiya, ko da ina kuka, ba zai daina ba".

 Stephen, a martanin da ya mayar, ya shaida wa kotun cewa yana son matarsa.
 
Ya kuma roki kotun da ta taimaka masa wajan kwantar wa da matan sa hankali, kada ta kashe auran.

 Stephen ya ce ya dade yana rokon matarsa ​​da kada ta nemi saki, domin a yanzu a shirye yake ya shawo kan yawan sha’awar jima’i.

A bayanin Mr Stephen, ya bayyana cewa "Na kai kawuna da abokaina gidan iyayenta (matarsa) domin in roke ta. Amma ta ki sauraron mu".

 Ya kuma roki kotun da ta ba shi lokaci domin sasantawa da matarsa.

 Alkalin kotun, John Dauda, ​​ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 6 ga watan Mayu domin jin ra’ayinsu da kuma sakamakon sulhun, yayin da ya shawarce su da su wanzar da zaman lafiya.

🖊️ Muhammad Isah Ramat

Ramat Unlimited 
Tuesday , 25th March 2025.

Comments

Popular posts from this blog

Sheikh Abdul Wahab bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi Inaugurated As 110th Ka'abah Guardian.

"Naheemah, Victim Of Collapsed Building In Lagos Left With Fake Promises By Lagos Government.

Shehu Sani Discribes Northern Politicians Visit To Buhari A Scam, And Plot To Unseat Tinubu In 2027